Gwamnatin Kano ta Kafa Kwamitin da Zai tabbatar Yan Kasuwar Kantin Kwari Sun bi Dokokin da akai Musu

Date:

Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar kwamitin karta-kwana domin bibiya tare da aiwatar da dokar hukumar gudanawar hukumar kula da kasuwar kantin kwari wacce majalisar dokokin jihar Kano ta yi.

 

Kadaura24 ta rawaito Da yake kaddamar da kwamitin, kwamishinan Kasuwanci cinika da masana’antu na jihar Kano Ibrahim Muktar ya ce an kaddamar da kwamitin ne domin kiyaye doka da gwamnatin jihar Kano ta yin a samar da hukumar kasuwar kantin kwari.

 

Ya ce anyi dokar karbar haraji da kuma aiwatar da wasu ayyuka da ma jagorancin kasuwar da nufin bunkasa harkokin kasuwanci.

Barista Ibrahim Mukar ya ce doka ce wani mutum ko wata kungiya ta rika karbar haraji a guraren yan kasuwa tare Kuma da rika bayyana wasu hanyoyi da za a bi wajen kasha kudaden.

Kwamishinan ya kuma bukaci yan kasuwa da su bawa kwamitin hadin kai domin samun nasara.

A jawabinsa Shugaban kwamitin kuma shugaban kasauwar kantin kwari Abba Muhammad Bello ya bada tabbacin za suyi duk mai yuwuwa domin sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.

Abba Muhammad Bello yace Gwamnatin Jihar Kano ta yi dokokin Dan musgunawa yan Kasuwar ba,sai don a tsaftace harkokin Kasuwanci da Kuma Kara Dora Kasuwar akan tsarin doka da oga da kuma tafiya dai-dai da Zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...