Daga Umar Mai Hula
Anyi Kira ga Al ummar musulmi dasu Mai da hankali wajen tallafawa marayu musamman a wannan hali da ake ciki.
Wannan Kiran yafito ne daga bakin Malam Muhammad yunusa Limamin unguwar tukuntawa a lokacin daya ke jawabi a wajen raba kayan karatu ga Marayu Guda 50 Waɗanda Gidauniyar tallafawa marayu ta Tukuntawa ta Gudanar.
Muna tallafawa Mata da Marayu ne don inganta Rayuwar su – Baba Yawale
Malam Muhammad yace akwai lada Mai tarin yawa da Allah yayi tanadi ga Waɗanda suke tallafawa marayu, Inda tallafawa marayu na Kara imani da Kuma Kara kusanci ga Allah.
Anasa jawabin shugaban kungiyar Yakubu Abubakar yace abin da yasa suka raba kayan karatun shi ne sabo da mahinman cin da karatu yake dashi a halin yanzu.
Yace Babu abun da zaka baiwa Mutum ka taimake shi3a Wannan Lokaci kamar karatu, yace shi yasa Muka Raba musu Waɗannan Kayan don su ji dadin yin karatunsu ba tare da Wani tarnaki ba.
Malam Yakubu yace da Gidauniyar su day dade da yin nisa wajen tallafawa marayu,Kuma ya Sha alwashin zasu cigaba da yin duk mai yiwuwa wajen tallafawa marayun don inganta Rayuwar su.
Suma marayun da suka rabauta da kayan karatun sunyiwa kungiyar fatan Al kairi da kuma Samun nasara.