Majalisar Matasa A Zamfara ta Zargi Gwamna Matawalle da Rashin Baiwa Matasa Kulawar data Dace

Date:

Daga Rabi’u Sani Hassan

 

Majalisar matasan Nigeria wato Youths Assembly of Nigeria reshen jihar Zamfara ta bukaci gwamnatin jihar da ta samar da muhimman tsare-tsare don inganta rayuwar matasan jihar domin samun makoma mai kyau ga matasan.

 

Kadaura24 ta rawaito Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka raba manema labarai mai dauke da sa hannun shugaban Kungiyar Mahmud A. Lawal, a cikin sanarwar Majalisar ta zargi gwamnatin jihar da taka muhimmiyar rawa wajen koma bayan da matasan jihar ke samu, sakamakon shakulatin bangaro da tayi da fannonin ci gaban su a 2021 data gabata.

 

Lawal yace a wannan shekarar ma hakan ka iya faruwa kuma zai zarce abun da ya faru a shekarar data gabata, duba da rashin wani muhimmin tanadi da gwamnatin ta yiwa matasan a cikin kunshin kasafin kudin shekarar 2022.

 

Ya kara da cewa ya kamata gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakai wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ýan kasa tare da samar da kyakkyawar makoma ga dubban daruruwan matasan jihar don gujewa gagarumar matsalar da ka iya tasowa nan ga a tsakanin matasan jihar.

 

Sanarwa tace kawo yanzu matasa da dama na fuskantar matsaloli da kalubale ta fuskoki da dama musamman yadda ýan bindiga suka addabi alúmmar jihar abinda yayin sandiyyar gurgunta harkokin tattalin arziki da tabarbarewar yanayi harkokin noma da Kasuwanci a Jihar.

 

Daga bisani shugaban matasan yace matsalar da harkar noma ta samu a jihar ya taka rawa sosai wajen rage yawan matasan dake iya samun damar shiga makarantun gaba da sakandire a jihar.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...