Yan Gudun Hijira a Zamfara na Cin Dusa don Su Rayu – inji Wata Mai Bada Agaji

Date:

Kungiyoyin ba da agaji a Najeriya sun ce rashin kulawar hukumomi ta jefa ‘yan gudun hijira da dama cikin mummunar rayuwa

Hajiya Maryam Aminu ta kungiyar Asshifa’a mai aikin ba da agaji ta fuskar lafiya ta ce da idanunta ta ga wata ‘yar gudun hijira ‘tana cin dusa domin babu abincin da za ta ci ta rayu’.

Ta kara da cewa a kwai matar da ta hadu da ita yayin da suke yin aikin agaji tana aikin surfe suna shan ruwan surfen ita da yaranta saboda ba su da wani zabi.

Ta gamu da yara masu yawa da ba sa samun kulawar kowa wadanda kuma suke fama da munanan rashin lafiya a inda suke zaune.

Wadannan labaruka marasa dadi na faruwa ne a inda yan gudun hijira ke zaune a unguwar Samu Naka da ke Jihar Zamfara.

Ko da yake wakilin BBC ya ce mutanen ba a sansanin ‘yan guydun hijira suke ba ko aka killace su, suna zaune ne a gine-gine da mutane suka fara ba a kammala ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...