Ku Daina Hadani da Wasu Gwamnoni a Ƙasar nan – Zulum ya Fadawa Yan Social Media

Date:

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roki masu kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni su daina.

Zulum ya yi rokon ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isa Gasau ya fitar ranar Litinin.

BBC Hausa ta rawaito Gwamnan ya yaba wa mutanen da ke tallata ayyukansa a shafukan sada zumunta, sai dai ya ce bai kamata a rika kwatanta “ayyukanna da na sauran gwamnoni ba, tun da dukkan jihohin suna da bambanci”.

“Duk da yake Ina matukar godiya bisa dukkan goyon baya da tallata ayyukana, a kwanakin nan, na samu sakonni, inda ake kwatanta ayyukan da muke yi a Borno da na wasu jihohi, a wasu lokutan ma ana zagi.

Gaskiya ba na jin dadi a duk lokacin da aka kwatanta ni da wani gwamna ta hanyar muzanta shi, musamman idan wadanda suke yin hakan suna cikin masu amfani da shafukan sada zumuntar da ke da alaka da mu”, in ji Gwamna Zulum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...