Yanzu-Yanzu: Gwamna Ganduje ya Sanya Hannu a Kasafin kudin Shekara ta 2022

Date:

Daga Zara Jamil Isa

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a yammacin ranar talatar nan ne ya rattaba hannu a Kasafin kudin Shekara ta 2022 wanda Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta Amince da shi.
Gwamnan ya Sanya hannun ne yayin taron Majalisar Zartarwar ta Jihar Kano Wanda ya gudana a dakin taro na Africa House.
Kadaura24 ta rawaito Jim kadan da Sanya hannu a Kasafin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Yan Majalisar bisa yadda sukai aikin kasafin kudin ba tare da Bata lokaci ba,Wanda hakan zai baiwa Gwamnatin damar Fara Amfani da Kasafin kudin a farkon sabuwar Shekara tunda ya Zama doka.
Gwamnan Ganduje yace yi mamakin yadda yan Majalisar suka kammala aikin nasu da wuri ba, Inda yace Zai tabbatar an yi aikin da Kasafin kudin kamar yadda Majalisar ta Amince da shi.
Ganduje ya yi alkawarin Cigaba da baiwa Majalisar yancin cin gashin kan Majalisar ba tare da tsoma Baki a harkokin aikin Majalisar ba.
Ya Kuma yaba da yadda Majalisar ta Gudanar da taron Jin ra’ayoyin al’umma,Inda ya bada tabbacin Kasafin kudin zai fi mai da hankali wajen kammala aiyukan da suka fara don gudun barin bashi Mai yawa ga Gwamnatin da zata gaje shi, Inda yace Kasafin kudin ya samu Kari daga Sama da Naira Biliyan 190 zuwa sama da Naira Biliyan 200.
A Jawabinsa tun da fari Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kano Hamisu Ibrahim Chidari yace sun Sami nasarar kammala aikin nasu ne akan lokaci Saboda yadda Gwamnan ya gabatar musu da daftarin Kasafin akan Lokaci.
Chidari yace Kuma dukkanin Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Jihar Kano sun bayar da duk wani hadin Kai ga kwamitocin Majalisar Wanda hakan ya taimaka wajen Samun nasarar aikin kasafin kudin kamar yadda doka ta basu dama.
Ya Kuma baiwa Gwamnan tabbacin Shugabancin Majalisar karkashinsa zai cigaba da baiwa bangaren Zartarwar Hadin kai domin Samun nasarar yiwa al’ummar jihar kano aiyukan cigaba.
Idan za’a iya tunawa a Ranar 28 ga watan October da ya gabata ne Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da daftarin Kasafin kudin Shekara ta 2022 a zauren Majalisar domin Gudanar da nasu aikin da dokar ta basu dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...