Daga Ibrahim Aminu Riminkebe.
Al’ummar garin Zangon Kabo dake yankin karamar hukumar Kabo a jihar kano, na cigaba da nuna farin cikin a sakamakon daukin da sanatan dake wakiltar Arewacin Kano wato Sanata Barau I Jibril ya Kai musu dauki ta hanyar kaddamar musu da aikin wata hanya mai tsahon tarinhin gaske data tashi daga Dugabau zuwa cikin garin na Zangon Kabo.
Wasu daga cikin yan asalin garin na Zangon Kabo da suke hadar da Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo, da Alhaji Dan Juma Liman Zangon Kabo da kuma Alhaji Bashir Abdulrahaman Zangon Kabo a yayin kaddamar da aikin hanyar suna masu bayyana cewar da zarar an kammala aikin hanyar suna da tabbacin cewar cigaba ta ko wacce fuska zai shigo cikin garin nasu, a sakamakon yadda garin na Zangon Kabo ke cike da manoma na damuna dakuma na rani ta yadda zasu jidadin fitar da amfanin gonakin nasu zuwa kasuwanni.
Kazalika hanyar zata kara saukaka musu matuka da gaske wajan fitowa da marasa lafiya zuwa asibitoci, ba Kamar yadda a baya ba suke shan wahala matuka da gaske kafin su fito daga cikin garin musamman a lokacin damuna.
A dan haka ne al’ummar garin na Zangon Kabo ke Kara mika godiyar ga sanata Barau I Jibril dama dukkanin wadanda suke da hannun wajan kaddamar da aikin hanyar garin nasu.
Da yake nashi wajan shugaban jamiyyar APC na karamar hukumar Kabo kuma wakilin Sanata Barau I Jibril daya jagoranci kaddamar da aikin hanyar wato Alhaji Hashim Abdulkadir Sarki ya tabbatar da cewar nan bada jimawa ba za’a kammala aikin hanyar domin cin moriyar al’ummar garin baki dayan su a sakamakon muhammancin da hanyar ke da ita.
Dan kwangilar da zai gudanar da aikin hanyar mai suna Alhaji Muhammad Sani Sarki yayi alkawarin yin aikin tsakanin shi da Allah Kamar yadda aka bashi amma, ya Kuma bukaci al’ummar dasu bashi hadin Kai domin ganin ya kammala aikin hanyar ba tare da an samu wata matsala.
Alhaji Alhasaan Liman Zangon Kabo wanda Kuma shine babban limanin Masallacin garin na Zangon Kabo ya bayyana cewar yau shekaru 60 da suke gabata suke fatan ganin anyi musu wannan hanyar data daga Dugabau zuwa cikin garin na Zangon Kabo a sakamakon muhammancin ta, amma Kuma ikon Allah yau da ran su da lafiyar suna ganin kaddamar da aikin hanyar garin nasu.