Rukayya Abdullahi Maida
An bukaci ‘yan Jarida dasu zamo masu yada labaran da zasu kawo zaman lafiya,tare da hada kan Al,ummar Jihar Kano.
Sarkin Kanuri Mazauna Jihar Kano Alh Mustapha Lawan me Kanon Borno, ya bayyana hakan ya yin da ya Karbi bakuncin Kungiyar Masu gabatar da shirin al’amuran Yau da kullum Wato Magazine programmes dake Jihar Kano a Fadar sa.
Sarkin Kanuri yace babu shakka ‘yan Jarida sune na farko da Suke hada kan Al,umma, Kuma Su na iya bakin kokarin su wajen kawo abinda Zai kawo cigaban kasa.
Inda yace lokaci ya yi da ‘yan Jarida zasu basu gudunmawa wajen hada kan duk al’ummar Kanuri da Suke rayuwa a Kano, tunda dai Shehun Borno shi ne ya bukaci hakan .
Alh Mustapha Lawan ya ja hankali Duk wasu bare-bari,Shuwa,Babur Manguno, da Sauran Al’ummar Jihar Borno da su zo domin hada kan su, tare da kokari wajen Samar da zaman lafiya .
Da yake nasa Jawabin Shugaban Kungiyar Masu gabatar da shirin Magazine programme dake Jihar Kano, Commared Sani Abdurrazak Darma ya bayyana cewa sun kai Me Kanon Borno ziyarar ne domin kulla alaka da Masarautar da ‘yan Jarida, tare da Sanar da Sarkin irin gudunmawa da Kungiyar take bawa Al’umma.
Sani Abdurrazak Darma yace tun lokacin da ake bukatar gidajen Radio su dinga tsaftace harshen su,, Kungiyar take Fadi tashin kowa ya bi doka.
Yayin Ziyar da Kungiyar takai Zuwa ga Masarautar Kanuri bisa Jagorancin Sarkin Kanuri Mazauna Jihar Kano Alh Mustapha Kungiyar ta zabe shi a matsayin Guda daga cikin Iyayen Kungiyar.
Kungiyar Radio Magazine ta samu tarbar daukacin Hakiman Masarautar Kanuri Mazauna Jihar Kano.