Ganduje ya Yabawa Abdulmumini Kofa Bisa Samar da Kasuwar da Zata Samawa Matasa Sama da Dubu Goma aikin yi

Date:

Daga Abdulrasheed B Imam

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa kokarin Sakataren Zartarwar na Hukumar Samar da gidaje ta Kasa kuma tsohon Dan Majalisar wakilai daya wakilci Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji Hon. Abdulmumini Jibril Kofa na Samar da Kasuwar da zata Samar da Aikin yi ga aƙalla Mutane Dubu 10 a Garin kofa dake Jihar Kano.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne Lokacin daya Kai Ziyarar ganin yadda Aikin ke gudana tare da zagaye dukkanin Rikunonin Kasuwar da katafaren Masallacin da Gidan man da aka Samar kusa da Kasuwar.
Gwamna Abdullahi Ganduje yace Samar da Kasuwar da Kofa yayi Zai taimakawa kokarin Gwamnatin sa na ganin Kano ta sake rike kambunta na Cibiyar Kasuwancin Arewacin Nigeria da wasu kasashen yammacin Africa.
Yace Gwamnatin sa tana aiki ba dare ba rana don haɓbaka Kasuwanci a Jihar kano ta hanyar sabunta Wasu Kasuwanni kamar Kasuwar kwari, shahuci da masallacin idi.
Ina Kira ga dukkanin ‘yan kasuwar dake Jihar Kano dasu yi saurin Zuwa su sayi shago a Wannan kasuwa domin in kuka bari aka bude ta baku samin shago a cikinta ba to Zan iya Cewa ka makara, domin kasuwace da tayi dai-dai da Zamani Saboda irin tsarin da akai mata.” Inji Ganduje
Ganduje ya yabawa Abdulmumini Jibril Kofa bisa Samar da Kasuwar,Inda yayi Kira ga Sauran Shugabanin da mawadata dasu Rika Samar da irin Waɗannan wuraren domin Samar al’umma aikin yi da Kuma saukaka Rayuwa ga al’umma.
A Jawabinsa Shugaban Hukumar Samar da Gidajen Kuma tsohon Dan Majalisar wakilai Hon. Abdulmumini Jibril Kofa ya ce ya samar da Kasuwar ne domin taimakawa al’ummar yankin Karamar Hukumar Bebeji dama Jihar Kano baki daya.
Kofa yace idan an bude Kasuwar aƙalla sama da Matasa dari biyar da za’a dauka aiki kuma a rika biyansu albashi duk wata, baya ga Sauran Waɗanda zasu rika harkokin Kasuwanci a Kasuwar Waɗanda yawan su ya haura dubu 10.
“Mun Samar da Kasuwa ta Zamani wadda mukai Mata tsarin na Zamani don Samar da gidan Mai , Gidan abinchi, bankuna masallaci da Makarantar Islamiyya da Boko, da dai Sauransu”.
Mai Girma Gwamna al’ummar Wannan yankin namu sun yi fice wajen noman tafarnuwa da citta don haka muka Samar da sashi guda a Kasuwar domin sarrafa tafarnuwar don fitar da ita zuwa kasashen waje”.  Inji Kofa
Hon. Kofa yayi fatan yan Kasuwa zasu je Kasuwar don mallakar shaguna domin cimma burin da yasa aka samar da Kasuwar na habbaka harkokin Kasuwanci a Jihar Kano da Arewacin Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...