Daga Kabiru Muhd Getso
Kwamishinan Aiyuka na jihar Kano Engr Idris wada ya kaddamar da kungiyar zurgazurgar Sufuri reshe jihar kano tare da bude masu sabon ofishi a harabar ma’aikatar ayyuka.
Engr idris wada ya bayyana cewa sufuri na da matukar muhimmanci ga rayuwar al’umma hakan tasa Gwamnatin jihar kano karkashin Shugabancin Dr Abdullahi Umar Ganduje a shirye suke domin bada gudummuwar da duk ya kamata don ha6aka sufuri a jihar Kano.
Shi ma a nasa jawabin sabon Shugaban Masu Zurga-zurgar ababan hawa na jihar kano Alh Lawan Isah Bubaram ya bayyan gansuwarsa akan yadda Gwamnati ke bada kulawa ta musamman akan harkar sufuri a kano, Sannan ya yi Kira ga sauran al’umma da su cigaba da bada cikakken hadin Kai akan sha’anin Sufuri.
Lawan Isah Baburam ya sha alwashin bin matakan da duk ya kamata domin ciyar da wannan kungiya gaba, tare da bijiro sabbun dabaru domin farfado da kungiyar tayi gogayya da sauran takwarorinta na jihoshi.
כחלק מהשירות, אנו מעניקים משלוחים בכל הארץ עד לבית הלקוח ושומרים עבורך על דיסקרטיות מלאה. דירות דיסקרטיות במרכז