Daga Zara Jamil Isa
Karamar hukumar Kumbotso ta kaddamar da wasu jami’an kula da tsaro guda 100 Karo na biyu da suka hadar da ‘yan sintiri da mafarauta a yunkurin ta na inganta tsaron yankin.
KADAURA24 ta rawaito Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hassan Garban Kauye Farawa shi ne ya sanar da hakan, yayin gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki akan al’amuran tsaron yankin, nan take Kuma ya baiwa kowanne daga cikinsu alawus na Naira dubu 20.
Farawa ya kuma kara da cewa karamar hukumar zata cigaba da baiwa jami’an kudin don inganta tsaro a yankin, wannan dai shi ne karon farko daya Fara shiga office bayan dawowarsa Daga kasa Mai tsarki yace,
“Zamu cigaba da Hidimtawa al’ummar karamar Hukumar kumbotso tunda mun lura wasu marasa kishi basason Haka, kayan Kumbotso na Yan Kumbotso ne”.a cewar Hassan.
Hakazalika farawa ya Kuma ja hankalinsu dasu cigaba da baiwa jami’an Yan sanda goyan baya gomin bunkasa harkar tsaro ganin yadda kullum karamar Hukumar ke Kara Tumbatsa.
Cikin wata sanarwa dauke dasa hannun Mai Taimakamasa Kan harkokin yada labarai Shazali farawa, ya Rawaito Shugaban na zayyana cewa nan bada dadewa ba, zai buzuro da wasu sabbin shirye shirye Domin bunkasa Rayuwar Al’umma, farawa dai ya Fara da Baiwa Yan sintiri 102 alawus din 20,000 .
כחלק מהשירות, אנו מעניקים משלוחים בכל הארץ עד לבית הלקוח ושומרים עבורך על דיסקרטיות מלאה. דירות דיסקרטיות במרכז