An aiyana Kamfanin Dangote Matsayin wanda yafi kowa tallafawa al’umma

Date:

Daga Zubaida Abubakar Ahmad
 An bayyana kamfanin Dangote a matsayin kamfani da yafi tallafawa al’umma a Kasar nan.
KADAURA24 ta rawaito Da yake mika lambar yabon ga kamfanin a karshen mako, shugaban kwamitin baje kolin kasuwanci na Cibiyar Kasuwanci ma’adinai da noma ta jihar Kano (KACCIMA) Alhaji Uba Tanko Mijinyawa ya ce kamfanin ya kasance a koda yaushe yana tsayawa tsayin daka wajen gudanar da ayyukan alheri ga al’ummar.
 Ya ce ba za a iya kididdige irin tallafin da kamfanin ya ke bayarwa ba, inda ya ce kyautar ta dace da Kamfanin na Dangote la’akari da irin hidimar da yake yiwa Jama’a.
Gungun Rikunonin Dangote ne ya bayar da kaso mafi yawa na daukar nauyin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa karo na 42 da aka kammala a Kano”. Ini shi
 Tun da fari Gwamna Abdullahi Ganduje, da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da jakadan kasar Uganda a Najeriya Ambasada Nelson Ocheger sai da suka yabawa shugaban kamfanin Aliko Dangote bisa yunkurinsa na bunkasa masana’antu a nahiyar Afirka.
 Darakta Janar na KACCIMA ya yi yabo mai yawa ga kamfanin na Dangote, inda ya kara da cewa “Mun yaba da kokarinsa (Dangote) da goyon bayansa ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka.”
 Ya kara da cewa kasashe takwas ne suka halarci bikin baje kolin kasuwanci na bana.  Kasashen Su ne: Indiya, Pakistan, Afirka ta Kudu, Singapore, Senegal, Masar, Mali da Kamaru.
 Wakilin kamfanin a kasuwar baje kolin, Alhaji Abdulsalam Waya ya ce kamfanin ya samu gagarumin ci gaba a fannin ayyukan jin dadi da wlawalar al’umma.
 A cewar Alhaji Waya wasu daga cikin ayyukan jin kai da Kamfanin Dangote ya gudanar a jihar Kano sun hada da: cibiyar aikin tiyata ta zamani da ke cikin harabar asibitin kwararru na Murtala Mohammed, Kano.
 Sauran, sun hada da: gina katafaren Makarantar Kasuwanci a cikin harabar Jami’ar Bayero ta Kano da ta kunshi dakunan taro, dakunan karatu, ofisoshi, ajujuwa da kuma dakin karatu, har da kuma gina gidajen kwana da samar da wasu ababen more rayuwa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, dake Wudil.
 Har ila yau,Bayan Gwamnati, kamfanin shi ne mafi yawan ma’aikata a Najeriya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...