Daga Zubaida Abubakar Ahmad
An bayyana kamfanin Dangote a matsayin kamfani da yafi tallafawa al’umma a Kasar nan.
KADAURA24 ta rawaito Da yake mika lambar yabon ga kamfanin a karshen mako, shugaban kwamitin baje kolin kasuwanci na Cibiyar Kasuwanci ma’adinai da noma ta jihar Kano (KACCIMA) Alhaji Uba Tanko Mijinyawa ya ce kamfanin ya kasance a koda yaushe yana tsayawa tsayin daka wajen gudanar da ayyukan alheri ga al’ummar.
Ya ce ba za a iya kididdige irin tallafin da kamfanin ya ke bayarwa ba, inda ya ce kyautar ta dace da Kamfanin na Dangote la’akari da irin hidimar da yake yiwa Jama’a.
” Gungun Rikunonin Dangote ne ya bayar da kaso mafi yawa na daukar nauyin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa karo na 42 da aka kammala a Kano”. Ini shi
Tun da fari Gwamna Abdullahi Ganduje, da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da jakadan kasar Uganda a Najeriya Ambasada Nelson Ocheger sai da suka yabawa shugaban kamfanin Aliko Dangote bisa yunkurinsa na bunkasa masana’antu a nahiyar Afirka.
Darakta Janar na KACCIMA ya yi yabo mai yawa ga kamfanin na Dangote, inda ya kara da cewa “Mun yaba da kokarinsa (Dangote) da goyon bayansa ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka.”
Ya kara da cewa kasashe takwas ne suka halarci bikin baje kolin kasuwanci na bana. Kasashen Su ne: Indiya, Pakistan, Afirka ta Kudu, Singapore, Senegal, Masar, Mali da Kamaru.
Wakilin kamfanin a kasuwar baje kolin, Alhaji Abdulsalam Waya ya ce kamfanin ya samu gagarumin ci gaba a fannin ayyukan jin dadi da wlawalar al’umma.
A cewar Alhaji Waya wasu daga cikin ayyukan jin kai da Kamfanin Dangote ya gudanar a jihar Kano sun hada da: cibiyar aikin tiyata ta zamani da ke cikin harabar asibitin kwararru na Murtala Mohammed, Kano.
Sauran, sun hada da: gina katafaren Makarantar Kasuwanci a cikin harabar Jami’ar Bayero ta Kano da ta kunshi dakunan taro, dakunan karatu, ofisoshi, ajujuwa da kuma dakin karatu, har da kuma gina gidajen kwana da samar da wasu ababen more rayuwa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, dake Wudil.
Har ila yau,Bayan Gwamnati, kamfanin shi ne mafi yawan ma’aikata a Najeriya.
Best Dating Sites for Real Relationships in 2022 click here