GAP ta yabawa Ganduje bisa nadin Lamin a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin kananan hukumomi

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
 Wata Kungiyar mai suna Grassroot Administration Platform (GAP) mai hedkwata a Arewacin Najeriya, ta yabawa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje bisa nada Lamin Sani Zawiya a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin kananan hukumomi da masarautu.
 Da suke yaba wa nadin a Cikin wata wasika da suka aike wa gwamnan mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar, David Samuel Gidanwaya, sun ce irin wannan nadin ya dace duba da kwarewar wanda aka nadan.
 Wasikar ta ce, “A matsayinsa na tsohon Shugaban kungiyar Shugabanin Kananan Hukumomi ta Jihar Kano (ALGON) tun daga Shekarar 2018 zuwa 2021 kuma tsohon Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa, nadin nasa ya nuna irin jajircewar Gwamnan wajen samar da ingantaccen tsari Gudanar da kananan hukumomi.”
 “Nadin Lamin Sani da Mai Girma Gwamna ya yi, wata alama ce da ke nuna cewa jihar Kano ta ba da muhimmanci sosai wajen ci gaban al’umma tun daga tushe,” a cewar wasikar.
 A sanarwar da Babban Sakataren yada labaran Gwamnan Malam Abba Anwar ya aikowa Kadaura24 yace kungiyar ta GAP Sun kuma bayyana cewa, tun a zamanin da Lamin Sani yake shugaban karamar hukumar Nassarawa suke bi sahun sa Kuma sun gamsu da irin cigaban da ya kai yankin.
 “Daga cikin shawarar da muka yanke, mun yi imanin Sabon Mai ba da shawar taimakawa wajen ciyar da kananan hukumomi yadda ya kamata zuwa mataki na gaba.”

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...