Ba Ranar da ba a Kashe Mutum a Arewacin Nigeria – Sarkin Musulmi

Date:

Sarkin Musulmin Najeriya Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar na ukku ya shawarci ‘yan Najeriya da su hada kansu don kawo karshen ta’addanci a kasar.

A lokacin da yake tsokaci kan matsalar tsaro a Najeriya a taron majalisar hadin kan addinai ta NIREC, Sultan Sa’ad Abubakar ya ce ba lokaci ba ne da mabiya addinai musamman Musulmi da Kirista za su rika zargin juna da yi wa juna barazana ba.

Sarkin Musulmin ya nuna damuwa kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jam’a ke ci gaba da afkuwa, amma kuma Musulmi da Kirista sun bige da nuna wa juna yatsa da yi wa juna barazana.

” Dole ne mu daina zargin juna kuma mu hada kai matsawar muna son mu yaki makiyanmu. Idan na ce zan yi magana kan rashin tsaro a arewa babu lokacin da za mu bar dakin taron nan. In ji Sultan.

Yakara da cewa , “yan kwanakin da suka wuce mun karanta a jaridu yadda aka kona matafiya a bas a Sokoto. Babu ranar da za ta zo ta wuce ba a kashe mutane a Arewa ba, musamman Arewa maso Yamma.”

Bugu da kari Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci shugabanni da sauran hukumomin tsaro su hada kai su kuma fahimci girman matsalar tare da magance ta.

“Kar mu yaudari kanmu, abubuwa ba sa tafiya yadda yakamata a Najeriya. Na sha fada a lokuta da dama cewa abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata. Kuma idan dai kasan matsalarka, magance ta ba zai yi maka wahala ba. Saboda haka ya kamata mu san na yi kafin lokaci ya kure mana

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...