Rundunar Yan Sanda a Jihar Katsina ta tabbatar da kisan gillar da aka yiwa kwamishinan kimiya da fasaha na Jihar Dr Rabe Nasir a gidan sa dake rukunin gidajen Fatima Shema a birnin Katsina, yayin da suka ce an kama mutum guda da ake zargi da aikata kisan.
Wannan ya biyo bayan ziyarar gidan sa da kwamishinan ‘Yan Sanda Sanusi Buba da Daraktan DSS suka yi, sakamakon samun labarin.
Rahotanni sun ce an dabawa kwamishinan wuka ne a ciki a cikin gidan sa, yayin da aka janye gawar sa zuwa ban daki inda aka kulle ta.
Kwamishinan ‘Yan Sanda Buba yace a daren jiya laraba aka kashe kwamishinan amma kuma sai yau alhamis aka samu gawar, yayin da yace an kama mutum guda da ake zargin yana da hannu wajen kisan.
Buba yace an dauki gawar kwamishinan zuwa Cibiyar kula da lafiya dake Katsina.
Bayanai sun ce jami’an tsaro sun samu wayar kwamishinan tare da wata da ake kyautata zaton na wanda ya hallaka shi ne.
Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari na daga cikin wadanda suka ziyarci gidan kwamishinan.