Sarkin Kano da Ganduje sun yabawa Dangote bisa shiga Kasuwar baje kolin Kano

Date:

  1. Daga Halima M Abubakar
5 ga Disamba, 2021.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yabawa Rukunin Kamfanin Dangote bisa yadda ya nuna kishi ya zo ya shiga baje kolin da ake gudanarwa yanzu a Jihar Kano.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana hakan ne Lokacin da ya ziyarci Rumfar Kamfanin Dangote dake filin baje kolin na kano Wanda shi ne karo na 42 Wanda ake gudanarwa duk Shekara a Kano.
 Sarki Bayero, ya bayyana jin dadin sa Kan yadda kamfanin ya samu rumfa a filin baje kolin, Mai Martabar yana tare da tawagar ‘yan majalisarsa da Jami’an KACCIMA, da kuma sauran Masu rike da sarautun gargajiya na Masarautar Kano .
 Sarkin ya kuma yabawa gwamnatin Kano, kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma (KACCIMA), da sauran kamfanoni da suka halarci bikin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa karo na 42 na Kano wanda za a rufe a ranar Asabar 11 ga Disamba, 2021.
 “Mun ziyarci bikin baje kolin kasuwanci, kuma mun yi farin ciki da ganin ci gaban da aka samu kawo yanzu duk da yanayin tattalin arziki da ake ciki a duniya.  Allah Ya taimake mu.”a cewar Sarkin
 Wata sanarwa da ta fito daga rukunin Dangote ta ce kamfanin ya sanya ranar Juma’a 10 ga Disamba, 2021, domin Mayar da ita Ranar Kamfanin ta musamman.
 Ziyarar Sarkin ta zo ne jim kadan bayan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci rumfar kamfanin inda ya yabawa Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote.
 Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan kasuwanci da masana’antu Ibrahim Mukhtar ya ce ba za a iya kididdige irin gudunmawar da Aliko Dangote ya bayar a Kano da ma Najeriya ba a fannin bunkasa masana’antu da samar da ayyukan yi ga al’ummar.
 Da yake jawabi tun da farko, yayin ziyarar da ya kai rumfar Dangote, jakadan Uganda a Najeriya, Ambasada Nelson Ocheger, ya bayyana Dangote a matsayin ‘Dan Afirka Mai kishi kuma ya bayyana shi a Matsayin wata cibiya, wadda ke ba da goyon bayan kai tsaye ga shugabannin Afirka ta fuskar samar da ayyukan yi da masana’antu Wanda hakan Kan yi tasiri ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar.
 Shugaban Cibiyar  Kasuwanci, masana’antu, ma’adinai da noma na Kano (KACCIMA), Dalhatu Abubakar, ya bayyana a matsayin wanda ya dace da taken kasuwar baje kolin karo na 42 na bana, wanda shi ne: Karfafa kalubalen da ke tattare da cutar ta Covid-19 don samun damar bunkasa da bunkasar kanana da matsakaitan masana’antu a Najeriya.
 Mataimakin shugaban Cibiyar ta KACCIMA kuma shugaban kwamitin baje kolin Uba Tanko Mijinyawa ya ce Kamfanoni Dangote sun kasance abokon hadin gwiwa a duk lokacin tsahon Lokaci, Sannan ya yaba da ayyukan agaji ta gidauniyar Aliko Dangote (ADF) take gudanarwa.
 Da yake zantawa da manema labarai tun da farko, Darakta Janar na KACCIMA Mustapha M. Aliyu ya yabawa Rukunin Dangote bisa hadin kai da daukar nauyin bikin baje kolin.
 A wata sanarwa da Kamfanin Dangote ya fitar ta ce kamfanonin da ke shiga baje kolin karkashin Rukunin Kamfanonin Dangote sun hada da: Dangote Cement, Dangote Sugar, NASCON, da Kamfanin Taki na Dangote.
 Rukunin Dangoten ya bukaci masu son yin siyayya  da duk wani reshen kamfanin, da su ci gajiyar irin wannan damar da Kamfanin ya bayar ta hanyar ziyartar Tebura na Musamman na Kamfanin a rumfarsa.
Sanarwa ta bayyana jihar Kano a  matsayin Cibiyar Kasuwanci tun a baya bama ga Nigeria kadai ba har ma da nahiyar Afirka baki daya.

5 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...