Karyewar Gada: Matafiya na Fuskantar Barazana a kan Iyakar Kano da Jigawa

Date:

Daga Kabir Muhd Getso
Al’umma da dama na kokawa bisa karyewar wata gada da ke iyakar Jihar kano da jigawa.
Wani matafiyi da Wakilin Kadaura24 ya zantawa da shi ya shaida masa cewar matafiya na shan bakar wahala a sakamakon lalacewar gadar, inda ta kai dole sai dai a gangara ta kasan gadar  abi ta cikin ruwa domin tsallakawa Wanda hakan kan haifar da lalecewar ababan hawa da dama.
Wasu mazauna yankin sun bayyana wahalar da matafiya ke sha a kokarin tsallaka wannan gada, sun kara da cewar tun kafin ta gagara hawa sunyi kira ga mahukunta amma ba’a samu nasarar kawo mata dauki ba. Don haka suke kira ga mahunta da su dauki kwakkwaran mataki akan wannan gada.
Shi ma shugaban karamar hukumar Birnin kudu dake Jihar Jigawa Hon Magaji Yusuf Gigo ya bayyana mana cewar duk da cewar wannan aiki na Gwamnatin tarayyar ne za su bi duk matakin da ya kamata wajen tuntubar ‘yan majalisu domin samun gudanar da wannan aiki cikin gaggawa.

15 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...

Kamata ya yi wajen Mauludi ya Zama waje Mai nutsuwa saboda ana ambaton Allah da Manzonsa – Mal Ibrahim Khalil

Shugaban Majalisar shuhurar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam...

Ra’ayi:‎Tsarin Kwankwasiyya ya dora Kano a gwadaben cigaba a mulkin Gwamna Abba Kabir -Adamu Shehu Bello

‎ ‎Ra’ayi ‎ ‎Daga Adamu Shehu Bello (Bayero Chedi), Jigo a Kwankwasiyya...