Daga Kamal Yakubu Ali
Shugaban Makarantar kamaludden Adamu Islamiyya Dr Adam Kamaludden Adamu na ma’aji yace babban Burinsu shi ne samar da ingantaccen ilimi da Tarbiyya ga mata da matasa.
Dr. Adam kamaludden Adam na ma’aji ya bayyana hakan ne a yayin bikin saukar karatun Alƙur’ani Mai girma Karo na shida na dalibai 89 Wanda ya gudana a farfajir makarantar Dake kusada Asibitin yara na marmara a kwaryar Birni Kano.
Dr Adam Yace samar da ingantaccen ilimi shi ne ginshikin cigaban kowacce al’umma adon haka suke bukatar goyan bayan iyaye domin cimma burin da suka Sanya a gaba.
Dr Adam ya bayyana godiyarsa ga Mai martaba sarkin Kano Alh Aminu Ado bayero bisa damar da ya samu na halarta bikin saukar karatun duba dabirin dumbin ayyukan da suke gabansa haka zaluka shugaban ya yabawa shugaban l karamar hukumar Birni faizu Alfindiki bisa gudunmawar da yake baiwa makaranatar.
A Jawabinsa Shugaban Karamar Hukumar Birni Fa’izu Alfindiki yayi alkawarin samarwa Makarantar gida domin fadada makaranatar don Kara inganta harkokin Ilimi addini Musulci a yankin.
Ya Kuma bukaci Iyayen Yara da su Kara dage damtse wajen tura ‘ya’yansu Makaranta tare da bibiyarsu , Inda Kuma ya bukaci Daliban da sukai saukar dasu dage da Neman Ilimi addini a fannoni daban-daban domin inganta Rayuwar su.
Shugaban Karamar Hukumar yace Karamar Hukumar ba zata yi Kasa a gwiwa ba Wajen cigaba da taimakawa makarantun Islamiyya dake Yankin domin samun Yara Masu Ilimi addini da Kuma tarbiyya.
wakilin Kadaura24 Kamal Yakubu Ali ya rawaito mana Cewa Gidan da Shugaban Karamar Hukumar yayi alkawari Zai siyawa Makamai gida ne Mai hawa biyu Wanda Kuma Zai taimaka wajen habbaka harkokin Ilimi a Yankin.