Tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd), ya ce dole ne kasashen Afirka su sauya salon da suke amfani da shi wajen wanzar da zaman lafiya yana mai cewa amfani da karfin soji ba zai kawo lumana ba.
Ya bayyana haka ne a Abuja ranar Asabar a wani taro da aka gudanar domin karrama shi.
Abubakar ya ce har yanzu nahiyar Afirka na fama da rikice-rikice “iri daban-daban,” wadanda ya ce suna ciki manyan kalubalen da ke addabar nahiyar.
BBC Hausa ta rawaito Jaridar ThisDay, wadda ta ambato shi yana wadannan kalamai ta ce tsohon shugaban kasar ya bukaci shugabannin Afirka su rungumi “sasantawa da yin sulhu” wajen magance rikici-rikice.