Tsaftar Muhalli: Kano zata dade Bata Manta da Sarkin Tsaftar Kano ba – Garban Kauye

Date:

Nasiba Rabi’u Yusuf
Shugaban karamar Hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban kauye farawa ya Aike da sakon Ta’aziyya ga Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da  masarautar Kano karaye da Kuma Al’ummar Jihar Kano Bisa Rasuwar Sarkin Tsaftar Kano Alhaji Jafaru Ahmed Sani Gwarzo.
Shugaban karamar Hukumar ta Kumbotso yace Za’a Dade ana tunawa da irin gudunmawar da Marigayin ya bayar wajen cigaban jihar Kano,  musamman ta fuskar Kiwon lafiya. Da yake Mika sakon Ta’aziyya Alhaji Hassan farawa yai fatan  Allah Swt ya jikansa yakai Rahama kabarinsa.
“innalillahi wa innalillahir Raji’un, Babu Shakka munyi Babban Rashi da fatan Allah Swt ya jikansa ya Kuma Baiwa Iyalai, yan Uwa da Al’ummar jihar kano Hakurin jure Rashi” a cewar Garban kauye.
Farawa ya Aike da sakon Ta’aziyya ne kai tsaye daga kasar Saudia Amadadin Al’ummar karamar Hukumar Kumbotso, Cikin wata sanarwa da Mai Taimakamasa kan harkokin yada labarai Shazali farawa ya sanyawa Hannu.
Kafin Rasuwarsa dai Gwarzo, ya kasance Babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Kan Tsaftar .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...

Kamata ya yi wajen Mauludi ya Zama waje Mai nutsuwa saboda ana ambaton Allah da Manzonsa – Mal Ibrahim Khalil

Shugaban Majalisar shuhurar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam...

Ra’ayi:‎Tsarin Kwankwasiyya ya dora Kano a gwadaben cigaba a mulkin Gwamna Abba Kabir -Adamu Shehu Bello

‎ ‎Ra’ayi ‎ ‎Daga Adamu Shehu Bello (Bayero Chedi), Jigo a Kwankwasiyya...