ICAN ta Fara wayar da Kan Daliban Sakandare muhimmancin Akanta, da Kuma tallafa musu

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Kungiyar kwararrun akantoci ta kasa reshen jihar Kano ta bukaci daliban dake Shirin zana jarrabawar  kammala sikandire da su hada hannu da kungiyar domin tallafa musu don Zama kwararrun akantoci.

 Shugaban kungiyar Abdullahi S Shehu ne ya bayyana hakan yayin da kungiyar ta ziyarci makarantar Tangaza dake kan titin Jami’ar Bayero domin wayar da kan dalibai a game da ayyukann kungiyar da Kuma tallafa musu da kayan karatu.
Malam Abdullahi Shehu yace  Samar da kwararrun akantoci daga tushe shi ne zai tallafa wajan   bunkasa rayuwar al’umma da Kuma basu damar dogaro da kawunansu ba tare da jiran aiki daga gwamnati ba .
 Shima Anasa jawabin Shugaban kungiyar kwararrun akantoci ta kasa reshen Kano da jigawa Dr . Abubakar Umar Faruk ya bayyana cewa dukkanin harkokin rayuwa na yau da kullum suna bukatar gudunmawar kwararrun akantoci, a don haka ya bukaci dalibai dasu hada hannu da kungiyar domin  ganin sun cimma burinsu na rayuwa .
Kungiyar ta bada tallafin kayan karatu ga makaranatar.
Da yake jawabin shugaban makarantar Tangaza Dr Bien ya yabawa kungiyar kwararrun akantoci ta kasa bisa zabar makarantarsu da suka yi domin basu tallafin kayan karatu da Kuma wayar da kan dalibai game da ayyukann kungiyar.
 Wakilin Kadaura24 ya bamu labarin cewa taron ya samu halarta Al’ummar da dama, inda daga bisani kungiyar ta Kai ziyat makaranatar Al-Amin dake unguwar Tal’udu domin mika tallafi da wayar dakan dalibai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Nigeria – Abba Anwar

Daga Abba Anwar Wani babban abin lura game da rayuwar...

Kungiyar Ɗaliban Mariri ta gudanar da aikin duba marasa Lafiya kyauta a yankin

Daga Abdallahi Shu'aibu Hayewa   Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato...

Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga...

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...