NNPC ta ce Yan Nigeria Zasu Sayi Litar Man Fetur Naira 320 Zuwa 340 a Shekara Mai Zuwa

Date:

Kasa da mako guda bayan da Hukumar Bada Lamuni ta Duniya ta baiwa gwamnatin Najeriya shawarar cire tallafin man fetur domin karkata kudaden da take zubawa zuwa ayyukan raya kasa, shugaban kamfanin man NNPC Mele Kyari yace farashin man na iya kaiwa naira N320 zuwa N340 kowanne lita daga shekara mai zuwa.

Yayin da yake gabatar da jawabi a Abuja, Kyari yace tabbas babu abinda zai hana cire tallafin man a shekara mai zuwa, domin kuwa dokar da ake amfani da ita wajen biyan tallafin zata daina aiki daga karshen watan Fabarairu mai zuwa.
Shugaban kamfanin man yace a shekara mai zuwa babu wani tanadi da akayi na sanya kudin tallafin, kuma ganin yadda ayyuka suka yiwa gwamnati yawa, zasu aiwatar da shirin janye shi a cikin sauki.
Dangane da tashin farashin iskar gas da ake girki da shi kuwa, Kyari yace batu ne na karuwar bukatar sa ta haifar da hauhawan farashin tare da karancin sa a kasuwannin duniya.
Shugaban kamfanin NNPC yace dama iskar gas bashi da wani tallafin da gwamnati take sanyawa, saboda haka farashin sa na tafiya ne da yadda kasuwar duniya take a koda yaushe.
RFI ta rawaito Kyari ya bayyana cewar kamfanin NNPC na iya bakin kokarin sa wajen kara yawan iskar gas din da ake sayarwa a cikin gida domin biyan bukatar masu aiki da shi.
Ita kuwa ministar kudi, Zainab Ahmed cewa tayi gwamnati zata cire tallafin domin baiwa ‘Yan Najeriya matalauta naira N5,000 kowanne wata a matsayin tallafin sufuri.
Ministar tace akalla ‘Yan Najeriya miliyan 30 zuwa 40 ake saran su ci gajiyar shirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...