Na Sami Darasi Mai yawa a Rasuwa Kanina Sani Dangote – Aliko Dangote

Date:

Daga Nura Abubakar
Shugaban rikunoni kamfanoni Dangote Kuma Wanda yafi kowa kudi a Africa Alhaji Aliko Dangote ya bayyana Cewa ya Sami darasi Mai yawa a Rasuwar kaninsa Alhaji Sani Dangote.
Aliko Dangote ya bayyana hakan ne Lokacin da ya karbi bakuncin tsohon Gwamnan Jihar Lagos Bola Ahmad Tinubu Wanda yaje don yayi Masa ta’aziyyar Rasuwar kaninsa Alhaji Sani Dangote a Gidansa.
Dangote yace kanin nasa ya rasu ne a gaban mahaifiyar su da shi Kansa da ‘ya’yansa a Kasar Amuruka ,” Muna gani na’urar da aka Sanyawa Sani tana nuna yake jikata ,Daga bisani ta nuna Cewa ba Zai wuce awa daya a Duniya ba Kuma Haka Muna gani ya rasu”. Inji Dangote
Yace mu Musulmi ne dama mun San Allah shi yake rayawa Kuma ya Kashe, Rayuwar kowa a hannunsa take sai dai akwai kowa ya kyautata alakar da Allah madaukakin Sarki.
A Jawabinsa jagoran jam’iyyar APC na Kasa Bola Tinubu ya yiwa mamacin fatan Allah yayi Masa gafara, tare da rokon Dangoten da su yi hakuri da Wannan Babban Rashin.
Yace Alhaji Sani Dangote za’a Dade ana tunawa da shi Saboda irin Gudunmawar da ya bayar wajen cigaban al’ummar Nigeria.
Bola Tinubu Lokacin da ya ziyarci Gidan Alhaji Aminu Alhassan Dantata Kaka ga mamacin yace Rashin Alhaji Sani Babban Rashi ne ba ga iyalansa Kadai ba har da Kasar nan baki daya.
“Kun yi Babban Rashi Amma Muna Masu baku Hakuri dama Allah yace duk Mai Rai sai ya mutu ,Yanzu Babu abun da Alhaji Sani yake bukata sai addu’ar” inji Tinubu
” Da kudi Yana hana mutuwa Babu shakka da daya Cikin attajirai sun sai Rai ,Amma Babu Wannan damar duk Wanda Lokacin da yayi dole sai ya Koma ga mahaliccin”. inji Tinubu
Yayin da ya Jawabi Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya godewa Bola Tinubun bisa ta’aziyyar da ya zo yayi musu.
Bola Ahmad Tinubu ya Kuma Ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero domin yiwa Sarkin ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Sani Dangote.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...