Zan yi Nazari Sakin Nnamdi Kanu – Buhari

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai yi nazarin buƙatar da ya kira “mai girman gaske” ta neman ya saki Nnamdi Kanu wadda ƙungiyar dattawan al’ummar Ibo suka gabatar masa.

Mista Kanu wanda ake zargi da aikata ta’addanci a gaban kotu, na hannun ‘yan sandan farin kaya na DSS sakamakon gwagwarmayar da yake yi ta neman kafa ƙasar Biafra a kudancin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin dattawan a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Mbazulike Amaechi.

“Kun nemi abu mai matuƙar girma a wajena a matsayina na shugaban wannan ƙasa. Tasirin buƙatar taku na da girma sosai,” a cewar Buhari cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar.

Ya ƙara da cewa buƙatar da dattijan suka nema “ta saɓa wa tanadin tsarin mulki da ya fayyace tsarin shugabanci tsakanin gwamnati da ɓangaren shari’a”.

“Sai dai buƙatar da kuka gabatar mai girma ce sosai amma zan yi nazari a kanta,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...