Rikicin APC a Kano: Tsohon mataimakin Ganduje ya sauya sheƙa zuwa ɓangaren Shekarau

Date:

 

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, a lokacin zangon mulkin gwamna Abdullahi Ganduje na farko, Farfesa Hafiz Abubakar ya bar tsagin gwamnan inda ya koma ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau.

Farfesa Abubakar, ya kasance mataimakin gwamna Ganduje daga shekarar 2015 zuwa 2018, inda a shekarar 2019 ya yi murabus tare da sauya sheƙa zuwa jam’iyar PDP, ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso da nufin tsayawa takarar gwamna.

Da ya fusata da zaɓen Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takarar PDP a zaben gwamna na 2019, Farfesa Abubakar ya fice daga PDP ɗin tare da komawa PRP.

A PRP ɗin ma dai haƙarsa ba ta cimma ruwa ba, in da jam’iyar ta baiwa Salihu Sagir Takai takara a zaɓen shekarar 2019, inda a bayan zaɓen ne sai kuma tsohon mataimakin gwamnan ya dawo tsagin Ganduje a ka ci gaba da tafiyar siyasa a ƙarƙashin jam’iyar APC.

Amma, bayan samun rabuwar kai a jam’iyar APC, inda aka samu ɓangaren Sanata Shekarau da ɓangaren Shekarau, an gaza sanin matsayar Farfesa Hafiz Abubakar, sai dai bayyanarsa a ka gani a taron da Shekarau ya shirya yau Talata a gidansa.

Yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a taron, Farfesa Abubakar ya ce ba abun mamaki bane a ganshi a taron saboda yana bin bayan duk inda gaskiya take.

A cewarsa, rikicin da yake damun APC a Kano ba abin jin daɗi ba ne kuma ya jefa jam’iyar cikin halin ni-ƴa- su da zai iya kawo mata tasgaro a zaɓen shekarar 2023.

Daily Nigeria ta rawaito Farfesa Hafiz ya koka kan cewa a tarukan siyasa, masu ruwa da tsaki na yawan yin shaguɓe da cewa jam’iyar ta mutane 3 ce, wato gwamna, matarsa da shugaban jam’iyya.

“Matsayata ita ce, ina alakanta kaina da gaskiya da kuma nan duba nan gaba. Maganar gaskiya ita ce abinda ke faruwa a APC ba abu ne mai dadi ba. A yau kowa ya sani cewa shugabbani a APC suna shiga taron jama’a suna cewa jam’iyya ta mutum uju cr- gwamna da matarsa da shugababan jam’iyya.

” Wasu lokutan muna ganin hakan abin dariya amma abinda muke gani a aikace yana nuna zahirin abinda ke faruwa. Jam’iyyar APC a Kano ta zama koma baya. Don haka yana daga cikin aikinmu mu ceto jam’iyyar mu ceto kanmu sannan mu ceci al’ummar Kano.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...