Yajin aikin ƴan garuwa ya haifar da tsananin wahalar ruwa a wata unguwa dake Kano

Date:

Daga Sani Danbala Gwarzo

 

Mazauna unguwar Rimin Keɓe da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo, Jihar Kano, sun wayi garin ranar Asabar da ibtila’in rashin ruwa sakamakon tafiya yajin aiki da masu saida ruwa a kura (ƴangaruwa) su ka tafi.

DAILY NIGERIAN HAUSA ta samu bayanai daga majiyoyi a unguwar, cewa, ƴan garuwan sun tafi yajin aikin ne sakamakon umarnin da shugabancin ƙaramar hukumar ya ba su na su cire duk wasu manyan bututun ruwa da su ka binne a ƙasa.

Majiyoyin sun ce ƙaramar hukumar ba ta jin daɗin yadda masu saida ruwan suka bibbinne bututun kai ruwan sabo da hakan ya sanya famfunan mutanen unguwar duk sun ƙafe, sai dai al’umma suna siya daga wajen ƴan garuwan.

Bayan wannan umarni ne sai ƴan garuwan su ka yi yunƙurin ƙara kuɗin jarkar ruwa daga naira 30 zuwa naira 70, lamarin da ya sanya al’ummar unguwar su ka ƙi amincewa.

Wani mazaunin unguwar mai suna Abubakar Tela ya baiyana irin mawuyacin halin da al’ummar unguwar su ka shiga.

A cewarsa, yanzu haka al’ummar unguwar sai dai su haura su samo ƴangaruwa daga wasu unguwannin, inda su ma su kai musu ƙarin kuɗi.

A halin yanzu fa sai ma su hali ne kaɗai ke iya siyan ruwan mai kyau a kan naira 70. Marasa hali haka suke haƙura su sayi ɗan naira 30 jarka kuma bashi da kyau ga ɗanɗanon sa kamar kanwa.

“Wasu ma fa fiyo-wata su ke siya su yi amfani da shi. Ka ga masu shan irin gurɓataccen ruwan nan ai suna fuskantar hatsarin kamuwa da cututtuka. A gaskiya mu na cikin mawuyacin hali,” in ji Tela

Tela ya yi kira ga gwamnati da ta kai musu ɗauki domin shawo kan matsalar.

A nata ɓangaren, wata fitacciyar ƙungiya mai zaman kan ta da ke taimakawa marasa ƙarfi, Creative Helping Needy Foundation, CHNF, tuni ta fara kai ɗauki da tankokin ruwa domin sauƙaƙawa al’ummar unguwar.

A wani taƙaitaccen saƙo da ta wallafa a shafin ta na facebook, Shugabar ƙungiyar, Fauziya D. Suleman ta ce sun yi amfani da kuɗaɗen tallafi da bayin Allah su ke baiwa ƙungiyar ne domin taimakon al’umma wajen siyan tankokin ruwa domin kaiwa zuwa Rimin Keɓe.

Yajin aikin da Ƴangaruwa su ka tafi a unguwar Rimin kebe saboda suna son kara kudin ruwa ya sa tsananin wahalar ruwa a unguwar, cikin irin kudin da bayin Allah ke tura mana mun saya mun samu damar siya musu yau, Allah ya sakawa masu taimakawa da alkairi amin,” in ji Fauziya

Ta kuma shaidawa DAILY NIGERIAN HAUSA cewa sun kai tanka ɗaya a ranar Asabar, za su kuma kai guda ɗaya a yau Lahadi, sannan gobe Litinin ma za su kuma kai guda ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...