Duk da nayi aure zan cigaba da fitowa a Fim din kwana 90 inji Rahma Mk

Date:

Daga Badiya Muhd

 

Masu kallo su na tsaka da shaukin kallon shirin fim mai dogon zango na Kwana Casa’in, kwatsam aka wayi gari daya daga cikin jaruman shirin fim Rahma Mk din ta yi aure.

Binciken da kadaura24 ta gudanar sun tabbatar da auren jarumar ,wanda aka daura  safiyar ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamban 2021.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, an yi shagalin bikin ne a gidan su da ke birnin Kano a sirrance don ba a bayyana wa mutane da dama ba.

Rahma Mk wadda ita ke fitowa a matsayin matar Bawa mai kada tsohon gwamnan jihar Alfawa a cikin shirin na kwana chasa’in.

Rahotanni sun nuna yadda aka yi shagalin bikin a gidan su da ke cikin garin Kano cike da sirri don ba kowa ya sani ba.

Tuntuni an samu labari a kan batun auren jarumar amma ba ta fadi lokaci da kuma wanda za ta aura ba, hakan ya sa mutane su ka dinga mamaki.

Yayin da manema labarai sun bukaci jin ta bakin jarumar,inda ɗ ta bayyana cewa:

“Dama na shaida cewa zan yi aure tun kwana 3 da su ka gabata, kuma ga shi Allah ya tabbatar kuma ya cika min buri na.”

Ta kara da addu’ar Allah ya ba ta haihuwa kuma ta yi fatan mutuwa a dakin mijin ta.

Batun fina-finai kuma ta ce za ta ci gaba da fitowa a shirin Kwana Casa’in, amma sauran babu tabbas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...