Rahotanni a jihar Kano na cewa ‘yan bindiga sun sace wani tsohon Janar-Manaja na hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa, NPA.
Bayanai sun nuna cewa an sace Bashir M Abdullahi daga gonarsa da ke kauyen Sitti na karamar hukumar Sumaila ranar Laraba da almuru.
BBC Hausa ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ba ta da labarin sace mutumin kawo yanzu.
Amma bayanai sun nuna cewa ‘yan bindigar sun rika fakon mutumin ne har suka kai ga sace shi.
Hakan na faruwa ne a yayin da rahotanni suke cewa wasu ‘yan bindigar da suka tsere daga jihohin Katsina da Zamfara da kuma Sokoto – wadanda suke fama da matsalolin tsaro – sun fara samun mafaka a wasu yankuna na jihar Kano.