‘Yan Bindiga sun Sace Malamai a Jami’ar Abuja

Date:

Rahotanni da cewa ‘yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari a Jami’ar Abuja, babban birnin kasar nan.

Wasu mazauna Jami’ar da ba sa so mu ambaci sunayensu sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar sun kutsa kai rukunin gidajen Jami’ar da ke Gwagwalada da misalin karfe daya na daren yau.

A cewar wani malami, an sace malamai guda uku da ‘ya’yansu biyu da kuma wani ma’aikacin Jami’ar.

Bayanai sun nuna cewa ‘yan bindigar sun ci karfin masu gadin Jami’ar sannan suka kutsa kai gidajen malamain suka sace su.

Har Kawo Lokacin hada wannna Rahoton Hukumomi basu ce komai ba Kan lamarin.

16 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...