Daga Sani M Sadeeq
Kwamitin karbar korafe-korafen zaben Shugabannin APC na jihohin da Uwar jam’iyyar APC ta Kasa ta aiko nan Jihar Kano ya Fara Zama a Ranar asabar din nan domin karbar korafe-korafen ‘ya’yan jam’iyyar Dangane da zaben.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban Kwamitin Dr Tony Macfoy yace Kwamitin Zai karbi korafin Waɗanda suka shiga zaben da aka gudanar a filin Wasa Sani Abacha ne Kawai Saboda shi uwar jam’iyyar ta Sani.
Yace Kwamitin Zai kawashe kimanin kwanaki uku yana Zama domin karbar korafe-korafen ,Wanda Zai Fara daga yau asabar zuwa Ranar litinin Mai zuwa, Inda yace zasu Rika Zama ne daga karfe goma na safe zuwa karfe hudu na Yamma.
Dr Tony yace su basu San da Wani zabe da akai a Wani waje ba a Kano bayan wanda aka gudanar a filin Wasa na Sani Abacha Saboda shi Jami’an uwar jam’iyyar APC ta Kasa Suka halarta har Suka saka da Rahoton su.
” Uwar jam’iyyar APC tasan da Wani zabe da akai Bayan wancan da kwanitoci biyu zata turo ,Amma Yanzu mu kadai aka turo Kano.“
Kwamitin Mai Mutane 5 dai yana Zama ne a sakatariyar jam’iyyar APC ta Jihar Kano dake Kan titin Maidugu a birnin Kano.
Idan ba’a mantaba a ranar Asabar din data gabata ne aka gudanar da zabuka biyu na Shugabanin jam’iyyar APC a Kano Wanda ya Samar da Abdullahi Abbas da Alhaji Ahmadu Haruna zago a Matsayin Shugabanin bangarorin jam’iyyar biyu a kano
Great article thank you for sharing!
online games for girls.
online games for girls Da dumi dumi Zamu karbi korafin zaben Your email address will not be published Required fields are