Da dumi-dumi: Zamu karbi korafin zaben APC da akai a Sani Abacha ne Kawai – APC ta kasa

Date:

Daga Sani M Sadeeq

Kwamitin karbar korafe-korafen zaben Shugabannin APC na jihohin da Uwar jam’iyyar APC ta Kasa ta  aiko nan Jihar Kano ya Fara Zama a Ranar asabar din nan domin karbar korafe-korafen ‘ya’yan jam’iyyar Dangane da zaben.

Kadaura24 ta rawaito Shugaban Kwamitin Dr Tony Macfoy yace Kwamitin Zai karbi korafin Waɗanda suka shiga zaben da aka gudanar a filin Wasa Sani Abacha ne Kawai Saboda shi uwar jam’iyyar ta Sani.
Yace Kwamitin Zai kawashe kimanin kwanaki uku yana Zama domin karbar korafe-korafen ,Wanda Zai Fara daga yau asabar zuwa Ranar litinin Mai zuwa, Inda yace zasu Rika Zama ne daga karfe goma na safe zuwa karfe hudu na Yamma.
Dr Tony yace su basu San da Wani zabe da akai a Wani waje ba a Kano bayan wanda aka gudanar a filin Wasa na Sani Abacha Saboda shi Jami’an uwar jam’iyyar APC ta Kasa Suka halarta har Suka saka da Rahoton su.
” Uwar jam’iyyar APC tasan da Wani zabe da akai Bayan wancan da kwanitoci biyu zata turo ,Amma Yanzu mu kadai aka turo Kano.
Kwamitin Mai Mutane 5 dai yana Zama ne a sakatariyar jam’iyyar APC ta Jihar Kano dake Kan titin Maidugu a birnin Kano.
Idan ba’a mantaba a ranar Asabar din data gabata ne aka gudanar da zabuka biyu na Shugabanin jam’iyyar APC a Kano Wanda ya Samar da Abdullahi Abbas da Alhaji Ahmadu Haruna zago a Matsayin Shugabanin bangarorin jam’iyyar biyu a kano

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...