Yan Sanda sun Kama Dan Bindiga Mai Shekaru 14 a Katsina

Date:

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta ce ta kama wani yaro ɗan ƙasa da shekara 20 da zargin shiga ayyukan ‘yan fashin daji da suka addabin yankin arewa maso yammacin ƙasar nan.

BBC Hausa ta rawaito a cewar kakakin ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, yaron mai shekara 14 ya amsa laifin kashe mutum biyu yayin wani hari da suka taɓa kaiwa.

“Yaron yana cikin waɗanda suka kai hari a Mallamawa cikin Ƙaramar Hukumar Jibia da kuma wasu a wajen Jihar Katsina, inda ya ce ya tuna lokacin da ya kashe mutum biyu,” in ji SP Gambo.

“Kuma ya shiga hare-haren da aka kai a Dankulumbo da Kukar Babangida, duka a Jibia. Sannan ya yi ƙwacen shanu da ba a tantance adadinsu ba.”

Ba kasafai ake kama yara ƙanana ba da zargin taimaka wa ‘yan fashin duk da cewa ‘yan sanda sun sha kama mata da kayayyaki a kan hanyarsu ta kai wa miyagun.

Har yanzu wasu sassa na jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da Neja – inda ‘yan fashin suka fi addaba da kashe-kashe da satar mutane – na cikin ɗaukewar layukan sadarwa, matakin da gwamnatoci suka ɗauka da zummar daƙile ayyukan maharan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...