Daga Sani Darma
Kwamishinan ‘yan Sanda yace aikin Jarida aikin Allah ne, Kuma ana samun lada a wajen Allah.
Inda yace aikin da Masu gabatar da shirin Al,amuran Yau da Kullum Suke yi abu ne Wanda jama,a Suke samun Ilimi da Hankali akan rayuwa.
Isma,ila Dikko ya bukaci Gidajen Radio dake Jihar Kano su cigaba da kokari domin cigaba da kawo shirye shiryen Zaman lafiya.
Anasa jawabin Shugaban Kungiyar Masu gabatar da shirin Magazine programme dake Jihar Kano, Commared Sani Abdurrazak Darma ,ya bayyana makasudin ziyarar da cewa .. domin kulla Alaka da kawo ci gaba ga masu gabatar a Shirin.
Sani Abdurrazak Darma yace Hadin kai da tafiya tare guri daya shine abinda Suke saka a gaba…tare da kawo cigaban Alumma.
Yayin ziyarar Kungiyar Masu gabatar da shirin Magazine programme dake Jihar Kano…Kungiyar ta Karrama Kwamishinan’yan Sanda Sama,ila Shu,aibu Dikko da Lambar yabo.
Karshen rahotan kenan Abdulmahid Habibb