Hukumar kula da yanayi ta Najeriya Nimet ta yi hasashen cewa za a yi sanyi na kwana uku tare da tsawa a fadin Najeriya daga yau Juma’a zuwa ranar Lahadi.
Nimet ta saki wannan sanarwa ne a ranar Alhamis a Abuja, za a dan yi hasken rana ran Juma’a da kuma gajimare a yankin arewacin Najeriya.
Ta kuma yi hasashen za a yi tsawa ta musamman a wasu yankunan adamawa da Taraba da safe.
“Da safe za a yi tsawa a Taraba da Kaduna da Bauchi da Gombe da kuma Adama, a wasu yankunan Borno da Yobe da Katsina da Jigawa da Zamfara da kuma Kano.