Bangaren su Malam Shekarau, tsohon gwamnan Kano ya zaɓi Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaban jamiyyar APC.
Sun yi zaben ne a wani wuri a Janguza da ke yankin ƙaramar hukumar Tofa.
Wannan na zuwa bayan ɓangaren gwamna Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano.
Bayanai sun ce tuni shugabannin ɓangarorin biyu suka yi jawabin amincewa da matsayin.
Hakan ya ƙara fito da ɓaraka tsakanin ƴaƴan APC a jihar Kano, yayin da jam’iyyar ke shirin tunkarar zaɓen 2023.
APC kano wuru wuru