October 19, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Majalisa ta yiwa Kasafin 2022 karatu na biyu

Kasafin shekara ta 2022 ya tsallake zaman karatu na biyu a gaban majalisar dattawan Najeriya.

An shafe tsawon sa’a guda da rabi a na muhawara kan kasafin da abubuwan da ya kunsa.

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din da ta gabata ya gabatarwa Majalisar kasafin da ya kunshi naira tiriliyan sama da 16.