October 19, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Akwai yiwuwar Sanatoci, Yan Majalisu, zasu kauracewa Babban taron APC na Kano

Daga Junaidu Khalid Gwadabe
Guda cikin jagororin jam’iyyar APC, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya yi wani babban taro a Abuja a daren jiya tare da wasu Yan Majalisu daga jihar Kano.
 Majiyarmu ta tabbatar da Cewa sun yi gabawar ne domin yin duba Kan makomarsu a cikin jam’iyyar APC Musamman a zaben Shekara ta 2023.
 Wadanda suka halarci taron sun hada da Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, Sanatan Kano ta kudu Kabiru Ibrahim Gaya, Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin Maliya, Dan Majalisar dake wakiltar Kananan Hukumomin D/tofa R/Gado Tofa Hon.Tijjani, Abdulkadir Jobe, Dan Majalisar dake Karamar Hukumar Birni Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada, Dan Majalisar dake wakiltar Karaye da Rogo Barr. Haruna Isa Dederi da Kuma Dan Majalisar dake wakiltar Kananan Hukumomin Gazawa da Gabasawa Nasiru Auduwa Gabasawa sai kuma Hon. Ahmad Haruna Dan Zago .
Har zuwa Lokacin hada Wannan Rahoton ba a bayyana makasudin taron ba, amma ana cewa suna shirin kauracewa babban taron APC mai zuwa ne Wanda za’a yi ranar Asabar 16 ga watan Oktobar da muke ciki.
Wani Wanda ya hadarci taron Kuma ya Nemi a boye sunansa ta ce sun tattauna ne Kan abun da ya Shafi yadda aka fitar da Waɗanda zasu jagoranci jam’iyyar ba tare da tuntubar Masu Ruwa da tsaki a jam’iyyar ba.
 Jam’iyyar APC a Kano tana fuskantar matsanancin rikicin cikin gida, inda wani bangare mai biyayya ga Sanata Barau Jibrin ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar idan ba a ba shi tikitin takarar gwamna na jam’iyyar ba.
 Manyan jiga -jigan Jam’iyyar da sukai taro ana hasashen zasu kauracewa Babban taron jam’iyyar don nuna rashin amincewarsu da yadda aka nisanta su daga cikin al’amuran da Suka shafi jam’iyyar.
Kadaura24 ta rawaito dama an dade ana ganin Kamar akwai Zaman doya da manja tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Gwamnan jihar kano, Inda a gefe guda ake ganin dama ta dade da yin tsami tsakanin Gwamnan da sha’aban Ibrahim Sharada Dan Majalisar dake wakiltar Karamar Hukumar Birni da Kuma Engr Tijjani Abdulkadir Jobe Dan Majalisar dake wakiltar Kananan Hukumomin D/tofa R/Gado da tofa .