October 19, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Akwai yiwuwar Buhari Zai sake Korar Ministoci

Akwai yiwuwar Shugaba Muhammadu Buhari ya sake korar wasu ministocin Najeriya bayan kammala taron bin diddigin ayyukansu da za a kammala yau a Abuja.

Taron na kwana biyu karkashin jagorancin shugaban kasar an soma shi ne a jiya Litinin domin bitar ayyukan ministocin da nasarorin da suka samu ko akasin haka.

Taron ya samu halartar dukkanin ministoci da manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati da manyan jami’a.

Buhari ya ce zai zauna har zuwa karshen taron domin sauraron bayanan kowanne minista da kuma nasarori da yanayin ayyukansu cikin shekaru biyu da suka gabata.

A lokacin gabatar da jawabinsa, Shugaba Buhari ya gargadi ministocin da manyan sakatarorin ma’aikatu su mayar da hankali wajen ayyukan da ya rayata a wuyansu domin ci gaban gwmanatinsa.

A watan Satumba shugaban ya kori ministocinsa biyu na noma da wutar lantarki kan rashin taka rawar gani a ayyukansu.

Kuma sun kasance ministocin farko da Buhari ya kora tun hawansa mulki a 2015.