October 19, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Har Yanzu Malam Ibrahim Khalil Muka Sani a Shugabancin Majalisar Malamai – inji Manyan Malaman Kano

Daga Halima M Abubakar

 

Jagororin Gamayyar kungiyoyin Malamai da Kungiyoyin addinin Musulunci na jihar kano sun yi watsi da Sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil Daga Shugabancin Majalisar Malamai ta jihar Kano.

 

Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne Cikin Wata sanarwa da Sakataren Kungiyar Dr. Sa’eed Ahmad Dukawa ya Sanyawa hannu Kuma aka rabawa Manema labarai a Kano.
Sanarwar tace wancan Mataki da aka dauka na cire Sheikh Ibrahim Khalil anyi shi bada Sanin jagororin ba, Kuma haka babu abun da Zai haifar sai fitina a tsakanin Malamai dama jihar kano daki daya.
Sanarwar ta bukaci al’umma suyi watsi da waccen Sanarwa da aka fitar tun da fari, Sannan Sanarwar tace sun dauki Wannan Matakin ne bisa Amincewa jagororin Qadirriyya da Izala dama Tijjaniya Kamar su:
Farfesa Musa Borodo, Sheikh Khalifa Karibullah Nasiru Kabara, Sheikh Abdulwahab Abdullah, Sheikh Ibrahim Shehu Maihula, Farfesa Muhd Babangida , Dr. Bashir Aliyu Umar, Imam Muhd Nasir Adam da Kuma Dr Mu’azzali Ibrahim Maibushira.
Daga Karshe sun tabbatar da Cewa har Yanzu Sheikh Ibrahim Khalil shi Suka Sani a Matsayin Shugaban Majalisar Malaman jihar Kano domin hakan ne Zai tabbatar da Zaman lafiyar da ake dashi a Kano.