Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo ƙasar nan bayan ya shafe wata kusan huɗu a birnin Landan sakamakon jinya.
Cikin wata sanarwa daga ofishin yaɗa labaransa a ranar Juma’a, Tinubu ya ce ya warke sarai tare da musanta “jitar-jitar da ake yaɗawa” kan rashin lafiyar tasa.
Ta ƙara da cewa an yi masa tiyata ne a gwiwarsa ta dama da kuma ba shi kulawar bayan tiyata.
“Mai girma Asiwaju Bola Tinubu ya sauka ne ranar Juma’a 8 ga watan Oktoba da yamma daga Landan,” a cewar sanarwar.
“Saɓanin abin da ake yaɗawa, ba a yi masa wata tiyata ba saɓanin wannan sannan kuma babu shirin yi masa wata nan gaba. Ya warke a kan lokaci kuma ba tare da wata matsala ba.”
Cikin sanarwar, Tinubu ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari “saboda ziyartarsa da ya yi a Landan” da gwamnoni da ‘yan majalisar yankin Arewa da ‘yan majalisar Jihar Legas.
An sha alaƙanta Bola Tinubu da neman takarar shugaban ƙasa a Najeriya, sai dai har yanzu dattijon mai shekara 69 kuma tsohon gwamnan Legas bai bayyana sha’awarsa ba ƙarara.
Веном 2 – смотреть онлайн в хорошем качестве https://bit.ly/venom2-2021