Shirin bunkasa Noma da kiwo na kano Zai sayi Kayan kula da lafiyar dabbobi na Naira Miliyan 60

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

Shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano, KSADP ya ba da kwangilar Naira Miliyan 60, 621, 500, don samar da kayan aiki rukuni na farko ga Ma’aikatan Kiwon Lafiyar dabbobi na garuruwa 220 .

Bayanin hakan na kunshe ne Cikin Wata sanarwa da Jami’in yada labaran Shirin Aminu Yasser ya Sanyawa Hannu Kuma aka aikowa Kadaura24.

Kayan sun ƙunshi kayan aikin dabbobi daban -daban, magungunan dabbobi iri iri, akwatunan Masu Rike sanyi, rigunan shiga dakin gwaje-gwaje, rigunan ruwa da Kuma takalma.

Sanarwar tace hakan na zuwa gabanin Fara Aikin bada horon yadda za’a gudanar da Aikin ga Masu kiwo don inganta lafiyar dabbobi a yankunan su.

Jim kadan bayan rattaba hannu kan kwangilar, wanda aka bai wa Kamfanin SUMAK General Merchants, Shugaban Shirin na jiha, KSADP, Malam Ibrahim Garba Muhammad ya bayyana cewa za a zabi Paravets biyar daga kowacce daga cikin kananan hukumomi 44 na jihar don samun horo na musamman, don ba su damar kula da lafiyar dabbobi.

“Masu neman aikin dole ne su kasance marasa aikin yi Kuma Waɗanda suka kammala karatun Karamar Diploma da Kuma babbar Diploma ko Waɗanda Suka gaba jami’a ko Masu Wata shaida a kimiyyar dabbobi, lafiyar dabbobi ko samar da dabbobi wanda za a horar da su kuma a ba su fakitin farko da ke kunshe da kayan aiki na asali da magunguna, don ba su damar isar da aikin kula da lafiyar dabbobi ga al’umma”.

” Za su kasance karkashin kulawar likitocin dabbobi daga Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar sannan kuma za su tsunduma don taimakawa a yakin da ake yi na rigakafin dabbobi a fadin jihar. Gabaɗaya, za su sa ido kan lafiyar dabbobi don hana barkewar cututtuka ”.

“Wannan yunƙurin yana da fa’ida mai yawa ga lafiyar ɗan adam don da samar da ayyukan yi ga matasan mu, waɗanda a cikin dogon lokaci za su horar da wasu su ma su kasance masu aikin dogaro da kai”.

29 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...