Ganduje ya Mika Takardar Shaidar Kama Aiki ga Sabon Sarkin Gaya

Date:

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci Mika katardar Kama Aiki bayan Sarkin ya karbi Rantsuwar Kama Aiki a gaban Gwamnan Kano.

Da yake jawabi Bayan rantsuwar Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Sabon Sarkin da yayi Aiki tukuru domin cigaban al’umma Masarautar Gaya.

Gwamnan yace akwai Bukatar Sarkin ya Maida hankali wajen inganta tsaro da tabbatar da yaran da suka Isa zuwa makaranta Suna zuwa da Kuma harkokin Lafiya don cigaban al’ummar Masarautar Gaya.

“Ina fatan Mai Martaba Sarki zaka baiwa gwamnatin jihar Kano hadin Kai a Dukkanin manufofin hidimtawa al’umma” . inji Ganduje

Gwamnan ya Kuma yabawa Sarkin bisa yadda ya rungumi Yan uwansa Wadanda suka nemi sarautar tare domin cigaban al’ummar sa. Ya Kuma yabawa Masu zabar Sarki na Masarautar Gaya bisa yadda suka gudanar da aikinsu ba tare da son Rai ba.

“Akwai aiyukan da muke gudanarwa na Daga darajar asibitin duk Masarautun da muke dasu don saukakawa al’umma da Kuma tabbatarwa Fuji Cewa wadannan Masarautun da muka Samar sun Zo Zama ne”. Inji Ganduje

Da yake jawabi Bayan Kama rantsuwar Sabon Sarki Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya godewa Gwamnan bisa yadda ya Amince da nada shi domin ya gaji Mahaifinsa.

Sabon Sarkin ya Kuma Bata tabbacin Zai Yi duk Mai yiwuwa wajen inganta tsaro Ilimi lafiya da dai Sauransu domin cigaban al’umma Masarautar Gaya.

“Ina bukaci al’ummar Masarautar Gaya su bani hadin Kai don muyi wa al’ummar mu hidima don cigaban su, Musamman ta fuskar Ilimi lafiya da kuma tsaro” inji Sarkin Gaya

Taron ya Sami halartar Sarakunan Rano karaye da wakilan Sarakunan Kano da bichi da hakimai da Sauran al’ummar Masarautar Gaya.

19 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NAHCON ta sanar da ranar da za a fara jigilar Maniyatan Nigeria zuwa kasar Saudiyya

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar kula da aikin hajji ta...

Hisbah ta rushe wajen da aka ce sawun Ma’aiki ya fito a jihar Kano

    Hukumar Hisbah ta kai samame tare da rushe wani...

ƴan siyasa ne su ka kashe Arewacin Nigeria — Inji Gwamna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ‘yan...

Shugaban Karamar hukumar Bagwai ya kaddamar da aikn gada ta sama da Naira Miliyan 160

Daga Shu'aibu Sani Bagwai   Karamar hukumar Bagwai a jihar Kano...