Ku Maida hankali ku koyin aiki don ku taimakawa al’umma -Phrm. Hisham ya fadawa Dalibai

Date:

Daga Nura Abubakar

Babban Darakta, Hukumar Kula da Magunguna ta jihar Kano, Pharmacist Hisham Imamudeen ya yi kira ga daliban Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jihar Kano da su kasance masu kyawawan halaye kuma su dage wajen ba da gudummawa don cigaban al’umma.

Pharm. Hisham ya yi wannan kiran lokacin da ya karbi daliban da aka tura hukumarsa don Sanin makamar Aiki.

Cikin Wata sanarwa da Jami’ar hulda da Jama’a ta Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano Hadiza M Namadi ta aikowa Kadaura24 Hisham yace kasancewar daliban a Hukumar Kula da Magunguna yana cikin tsarin karatun su don haka ya bukaci su sadaukar da kai wajen amfani da damar don haɓaka ilimin su.

Babban Darakta ya lura cewa girmamawa, biyayya su ne Manyan abubuwan da ake Bukata ga Masu neman manin kwarewa domin Samun Nasara.

Don haka ya gargade su kan su guji yin duk wata hulda da miyagun kwayoyi wanda ya ce hakan shi ne babban abin da yafi haifar da matsala a rayuwar kowanne Dan Adam.

DG ya kuma shawarci daliban da su kasance jakadu nagari ga makarantarsu da Kano a duk inda suka tsinci kawunansu.

A nasa jawabin, wakilin daliban Mansur Magaji, Wanda yayi Jawabi a madadin daliban, ya gode wa DG bisa karimcin da ya nuna musu da nasiha sannan ya yi alkawarin zasu yi aiki da shawarwarin da Kuma maida hankali wajen koyon aiki.

24 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...