Dogaro da Kai: Hon.Doguwa Ya baiwa Matasa 200 tallafin Naira Dubu Hamsin kowannesu

Date:

Daga Zara Jamil Isa

Dan majalisar mai wakiltar Doguwa/Tudun-Wada kuma shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Honorabul Alhasan Ado Doguwa ya yi kira ga matasa a mazabarsa da su yi amfani da damar da aka ba su don su zama masu dogaro da kawunansu Maimakon jiran babban Aiki.

Kadaura24 ta rawaito Cewa Da yake jawabi a wajen bikin yaye matasa 200 da aka koyawa sana’o’in daban-daban a garin Tudun wada a ranar Litinin, Dan Majalisar ya ce za a ci gaba da gudanar da aikin kamar yadda aka fara da matasa maza da mata 200.

Doguwa wanda ya samu wakilcin mataimaki na musamman kan harkokin gudanarwa, Alhaji Hassan Inuwa Riruwai ya ce an tsara wannan tallafin ne don tallafawa matasa marasa aikin yi don a kowa musu sana’o’in Dogara da Kai domin suma su sami damar bada tasu Gudunmawar wajen bunkasa tattalin arziki da Rayuwa al’ummar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun-Wada da kasar gaba daya.

Ya jaddada cewa tallafin Zai Magance Matsalolin Rashi Aikin yi ga Matasan Yankin don cigaban Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada.

Bikin wanda ya Sami halartar manyan mutane da kuma fitattun yan siyasa a yankin wanda suka haɗa da shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolin Doguwa da Tudun Wada, wanda kuma ya samu halartar Hakimai na Doguwa da Tudun Wada da har ma da Wamban Rano.

Wasu daga cikin Waɗanda suka ci gajiyar tallafin Nasiru Ali daga Garin Burum-Burum da Hauwa isa sun yi alƙawarin yin amfani da dubu hamsin – hamsin din da aka basu don fara kasuwanci.

15 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...