Na yi Matukar Kaduwa da Rasuwar Sarkin Gaya – Sanata Kabiru Gaya

Date:

Daga Abdulrasheed B Imam

Sanatan Kano ta kudu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana matukar kaduwarsa da rasuwar Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir a Ranar Larabar nan.

Sanata Kabiru Gaya ya bayyana hakan ne Cikin Wani sakon ta’aziyya da ya Sanyawa Hannu Kuma ya aikowa Kadaura24.

Sanata Gaya yace Rashin Sarkin Babban rashi ne ba ga al’ummar Masarautar Gaya kadai ba ,har da jihar Kano da Nigeria baki Daya.

” Mai Martaba ya taimaki al’umma sosai tun da kuruciyarsa Lokacin yana Abuja ya samarwa Mutane aiyukan yi Kuma har ya zama Sarki Bai daina ba. Kuma da ya Zama Sarki Mai cikakken iko yayi iya Bakin kokarin wajen Samar da Zaman lafiya bunkasa Ilimi lafiya da dai Sauransu.” Inji Sanata Kabiru Gaya

” Alhaji Ibrahim Abdulkadir mutumin kirkine Wanda ya sadaukar da Rayuwarsa wajen hidimtawa al’ummar sa da Kawo Cigaba yankinmu Kuma ya taima sosai wajen inganta Rayuwar Al’ummarsa”. Inji Sanata Gaya

Sanata Gaya ya Mika Sakon ta’aziyyar ga Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Sarakunan jihar Kano da al’ummar Masarautar Gaya da na Kano Baki daya

Yayi addu’ar Allah ya gafartawa Mai Martaba Sarkin yasa Yana aljanna ya Kuma kyautata makwancinsa .

18 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Maikwatashi: Tsohon kwamishinan Ilimi ya rubutawa gwamnan Kano budaddiyar Wasika

Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Sanusi...

Gwamnatin Kano ta sauyawa makarantar mata ta Mai Kwatashi matsugunni

Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ɗauke Karantar Sakandare...

Sule Lamido, Ya Yi Barazanar Maka Shugabannin PDP a Kotu

  Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana...

Tsofaffin Kansiloli Sun Yi Saukar Alƙur’ani da Addu’a na Musamman ga Gwamna Abba

  Ƙungiyar tsofaffin kansiloli na jihar Kano ta gudanar da...