Daga Rabi’u Usman
Gwamnatin Jihar Kano ta Tabbatar da Alhaji Shehu Rabi’u a Matsayin Halastaccen Kwamandan Rundunar Vigilantee na Jihar Kano.
Wannan na Zuwa ne Bayan Kwanaki 58 da Rasuwar Babban Kwamandan Rundunar Muhammad Kabir Alhaji *(M K ALHAJI).*
A Wannan Ranar dai Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano Hon Murtala Sule Garo ne ya Mika masa Takardar Shaidar kama Aiki a Matsayin Babban Kwamandan Rundunar Vigilantee na Jihar Kano a Wannan Rana.
Jim kadan da Mika Masa Takardar Shaidar kama Aiki ne Muka Zanta da Sabon Kwamanda Alhaji Shehu Rabi’u a Matsayin Halastaccen Kwamandan Rundunar Vigilantee na Jihar Kano, Inda ya Mika Godiyar Sa ga Allah Madaukakin Sarki da Kuma Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya Bisa Amincewa da yayi na tabbatar da Shi a matsayin Kwamandan Vigilantee na Jihar Kano.
Daga Nan yayi Kira ga Al’ummar Jihar Nan dasu Kasance Masu Taimakawa Jami’an Rundunar Vigilantee da Kayan Aiki harma da Basu Bayanan Sirri da Zarar Sunga Motsin Abin da Basu Amince da Shi ba Don Kawo Musu Dauki na Gaggawa.
A Nasa Bangaren Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano Murtala Sule Garo ya Mika Takardar a Madadin Sa, inda ya Tabbatar da Cewar Shehu Rabi’u ya Chancanci ya Rike kujerar sakamakon tun a Baya Kafin Rasuwar M K ALHAJI Shi ne Mataimakin Kwamandan Rundunar Vigilantee Sashen Kula da Ayyuka na Musamman (Operations Commander).
Inda ya Bukaci da ya Kasance Mai Kula da Dukkannin Shige da fice na Mutanen da Ba’a yarda da su ba a Fadin Jihar Kano baki daya Domin Dakile Matsalar tsaro a Fadin Jihar Kano.
Where to buy steroids | Where to buy real steroids online forum? https://wheretobuysteroids2022.wordpress.com