Al’ummar Kano Sun Yaba da Samuwar Kasuwar Dalar Gyada a Kano

Date:

Daga Sajida Sulaiman

Biyo bayan Wani taro mai cike da tarihi wanda ya ja hankalin wani shahararren attajirin dan kasuwa a birnin Kano, kan hanyoyin farfado da martabar Kano a matsayin cibiyar kasuwanci Arewacin Nigeria, yanzu haka shahararriyar kasuwar Dalar Gyada wadda MN ATAJ CONSTRUCTION LIMITED AND AVENTURES INDUSTRIES suke ginawa an yaba da gina ta a cikin birnin Kano kuma an itifakin zata samu karbuwa da fa’ida sosai wajen cigaban Kasuwanci a Kano.

Hamshakan attajiran yan kasuwa waɗanda suka taru a dakin taro na Meenat, yayin taron an yi ittifaƙi tare da cewa Babbar kasuwar zata taimakawa dubunnan al’umma Masu son yin siyayya tare da sauƙaƙa musu, duba da tsarin da akai wa Kasuwar wajen gina manyan kantuna, da Kuma banki don sauƙaƙa al’umma.

Duk da haka manyan ‘yan kasuwa sun lura cewa Kano tana kan hanyar samun daraja, shahara a fannin kasuwanci saboda Kasuwar ta ƙunshi duk wasu abubuwan more rayuwa da ake buƙata Wanda zasu jawo hankulan ma masu yawon bude ido da Masu zuba hannun Jari daga kasashen waje don bunkasar Kasuwanci.

Sai dai ra’ayin wani mashahurin ɗan kasuwa a Kano, wanda ya nemi a sakaye sunansa yace kasuwar ta zo ne a daidai lokacin da kasuwanci a Kano ke buƙatar farfaɗowa da gaggawa don a sami wadataccen arziki da kuma share fagen ci gaba da harkokin kasuwanci.

mamallaka wuraren kasuwanci a kano bisa ga ra’ayin mutane, shine babban goyon baya da taimakon da ake buƙata don yin fice a cikin ƙoƙarin sanya Kano ta zama tushen ci gaban tattalin arziƙin da zai iya canza rayuwar mutane ta kowane fanni.

Daga Karshen taron an tsimma matsayar cewa dole sai an sanya manyan hamshakan ‘yan kasuwa Cikin Masu Masu Zartarwa ko Masu fada a aji a harkar, Inda aka ce hakan ne kawai Zai farfado da harkokin Kasuwancin, tare yabawa kyakkyawan hangen nesa na masu mallakar Kasuwar Dalar Gyada don zata taimakawa cigaban Kasuwa da yan Kasuwa a Kano.

Taron ya Sami halartar Alhaji Aminu ahmad Mai turare, Alhaji sabiu Bako, Alhaji Bature, Abdulaziz, Alhaji Bashir othman Tofa, da Engr. Rabi’u Sufi Wanda shi ne ya wakilci Kamfanin MNTAJ CONSTRUCTION LIMITED AND AVEMTION INDUSTRIES da dai sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...