Yan Sanda a Kano sun Kama barayin Jaririyar da aka sace a Asibitin Nasarawa

Date:

Daga Nura Abubakar

Rundunar Yan Sanda ta Kasa reshen jihar Kano ta bayyana Cewa tayi Nasarar Kama Mutane da ake zargi sun Sace Wata Jaririya a asibitin Nasarawa daka Kano a Ranar Larabar data gabata.

Kadaura24 ta rawaito Cikin Wata sanarwa da Jami’in hulda da Jama’a na Rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar yace sun Nasarar Kama Mutane biya Mata da miji Maryam Sadiq Mai kimanin Shekaru 22 da Mai Gidanta Abubakar Sadeq Mai Shekaru 50 mazauna unguwar Rijiyar Zaki dake Kano da Jaririyar.

Sanarwar tace Bayan Samun Rahoton batar Jaririyar ne kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Sama’ila Dikko ya bada Umarnin nemo Jaririyar Kuma Cikin ikon Allah an ganota Bayan Bincike da Jami’an Yan Sanda suka gudanar.

Kafin Kama Matan da mijin har sun Shirya shagalin Bikin suna Saboda samun Jaririyar,Amma Daga bisani makotansu suka fadawa Yan Sanda kasancewa basu San matar da Cikin da har ta haifi yarintar ba.

Sanarwar tace tuni dai aka Mika Jaririyar ga Iyayenta, Kuma kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Sama’ila Dikko ya bada Umarnin Mika lamarin ga Sashin Binciken Manya laifuka na Rundunar don cigaba da Bincike.

4 COMMENTS

  1. Will what I say be heard? Is it worth spending the time making a comment if it’ll be lost amongst the many that have already been written?
    Maybe you can write a post about encouraging people to join conversation that is already quite busy or even a post about being heard among dozens of other voices that are commenting.
    카지노사이트

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...