Kungiyar Masu POS ta Fara tan-tance Masu POS a Kano

Date:

Hadaddiyar Kungiyar Masu Hada Hadar Cirar Kudi na POS ta Kasa Reshen Jihar Kano da ake Kira Association of Mobile Money Operators of Nigeria (AMMON) Karkashin Jagorancin Shugaban Kungiyar Comrade Salihu A Umar Sun Gudanar da Zagayen tsabtace harkar Huldatayyar POS a Jihar Kano tare da Babban Bankin Kasa na CBN.

Bayan kammala Zagayen ne Muka Zanta da Salihu Umar Inda yace ya Zama Wajibi Kowanne Mai Sana’ar POS ya Kasance Mai bin Doka da Oda Wajen Gudanar da Sana’ar Sa Domin Samun Kwanciyar Hankali ga Masu Mu’amalantar su.

Yana Mai Cewar akwai Hanyoyi da Dama da Mutane Zasu Ajiye Kudaden su ba tare da an Samu Matsalar da Zata Shafi Ajiyar Su ba, ya Kara da Cewar da Zarar an Samu Wani ya Zambaci mutum Zasu Dauki Matakin Ladabtarwa a Kan sa.

Daga Nan yayi Kira ga Jama’ar da Suke Mu’amalantar Masu POS da su Kasance Masu Hada Karfi da karfe Wajen Kawo Cigaba a Jihar Kano Dama Kasa baki daya ta Fannin Samar da Guraren Cirar Kudi a Maimakon Zuwa Bin Dogon layi na Banki.

Wakilin Kadaura24 ya Ruwaito Mana Cewa, daga Cikin Guraren da Kungiyar ta Zagaya Sun Hadar da Unguwar Sheka, Zoo road, Shagari Quarters, Hausawa da Sauran Su.

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...